Sunday, September 3, 2023

HUSSAINI ZAMANI

 Duk ƙasar da take da tsayayyen bawan Allah Bahussaine, da al'umma wacce ke ƙoƙarin kwatanta Husainanci (Tashi tsaye a ce wa zalunci da azzalumi kule), toh wannan ƙasar ta na da fata. Allahumah Thabit Aqdamana.


Shareef Haji Bahador


Saturday, September 2, 2023

ZIYARAR MAKWANCIN SHIHIDAN TATTAKI

 DAGA TASKAR SHUHADA




 Shahidanmu   na Yaumu Arbaeen,  shekara bakwai kenan, wanda  gwamna  Ganduje  yasaka  aka kashe a kwanar  Dawaki.

Friday, September 1, 2023

GWARAZANMU SHAHIDANMU








 Cikin hotuna taron tunawa da ranar haihuwan Shahid Muhsin Badamasi wanda ya gudana da yammacin yau Juma'a a makwancin Shahidai dake Darur Rahma Dambo Zaria.......

Wednesday, August 30, 2023

SHAHIDAN TATTAKI


 Shahidan Tattaki nafarko daga yankin kano waɗanda Jagora Sheikh Ibrahim Zakzaky (H) yayi masu Sallah a Hussainiyya Baqiyyatullah Zariya.

SHAHIDANMU GWARAZAN MU








 Taron Tunawa Da Shahadar Shaheed Ali Bodinga


An soma taron tunawa ranar shahadar shaheed Ali Haidar musa Bodinga shekara 2 da shahada a karo na 2 a muhallin Madrasatul fudiyya Bodinga wanda ake gabatarwa a yau Laraba 31 gawatan August 2023.


Photo:

 Faisal A Imam 

Muhammad Bello

Daga: Halidu Shaheed Usman

WASIYYAR SHAHIDAN MU



 DAGA WASIYYAR SHAHEED MUHAMMAD SANI(ASA)🌹


Jinjina ta musamman da girmamawa ga shugabana sayyed Ahmad zakzaky(H). Da shahidan Abulfadl da suka bada ransu wajen kare jagora.


Wata jinjina ga gwarazanmu na jaishu Ahmad wato shihadanmu.kasatan irinsu shahid ukasha lastdon da shahidanmu da abuja struggle irinsu shaheed Ahmad rufa'i dodo. 


Bayan mila gaisuwata, ina maimuku wasiyya yaku yan uwana masoyana kuma abokan aiki. Cewa idan kukaji labarin shahadata ta riskeku inamai muku wasici da wadannan abubuwan.


Da farko musani tun ba'a haifemuba iyayenmu suka taso suna wannan gwagwarmaya har Allah yasa aka haifemu muka taso, da tsayawarsu shaheed Ahmad muka fahimci aikin da yake gabanmu muka tsaya  muka fara wani abu.


Hakikanin gaskiya munsamu kanmu cikin yanayin da muntabka kuskure anan waki'an 12 december na gyallesu, saboda a rashin tsayawa muyi abunda ya dace aka kai ga su sayyed(H) har aka kai halin damuke ciki yanzu.


Inamuku wasiyya ku rike Abuja struggle  hannu bibiyu ku tsaya kugani kunyi abunda ya dace domin ganin cewa mun wanke wancan zunubin da mukayi abaya.


Sannan ina maimuku wasici da abokan aikina, wanda aka fadi tare aka tashi tare akayi abuja struggle akasha wuya sosai aka kuma ji dadi tare. 


Inamuku wasici da a tsaya kyam akan tafarkin Allah, ita kisa bata karamana komai sai dai ta karamana kumaji akan abunda muke, sannan furucin kisa baya karamana komai sai shaukin shahada.


Munsani dama mu an haliccemu ne don mu mutu, in Allah ya tashi zai mana kyauta ta musamman, sai yamana da Shahada.


Muna fatan Allah ya dawo dasu lokacin bayyanar imamul hujja a karkashin tutarsa.


___Ahmad wulaya

 https://www.facebook.com/profile.php?id=61550291393124

HUSSAINI ZAMANI

 Duk ƙasar da take da tsayayyen bawan Allah Bahussaine, da al'umma wacce ke ƙoƙarin kwatanta Husainanci (Tashi tsaye a ce wa zalunci da ...